Tsokaci Akan Akan MaKiyan Jarumi Adam A Zango
Ban Sani ba ko mutanen da ke jifan zango da munanan Kalamai, kazafi da ‘kage ko su na da Garantin cewa su shiryayyu ne, wadanda ke da tabbacin cikawa da Imani a karshen rayuwar su.
Akwai Hadisin maaiki saw da ke cewa, dayan Ku zai kasance yana aiki irin na Yan aljanna,har sai ya kasance tsakanin sa da shiga Aljanna bai fi Zira’i ba, sai ya aikata aiki irin na yan wuta kuma sai ya shige ta. Haka da dayan ku zai kasance yana aikata aiki irin na Yan wuta har sai ya zama Zira’i ne tsakaninsa da wutar, sai kuma ya aikata aiki irin na Yan Aljanna. Sai kuma ya shiga Aljannar. Kodayake wasu na raunana ingancin Hadisin,
amma yana faruwa a rayuwa. Mutum ya taso cikin Sabawa Allah daga karshen rayuwa sai a ga shiriya ta zo ma sa. Wannan Hadith yana koyar da mu dagewa kan bautawa Allah Madaukakin Sarki. Yana kuma nuna mana mu zama cikin takatsantsan domin rayuwar ba ta da tabbas.
Wani abu da ya taba faruwa da gaske a wani gari ya ba kowa Mamaki,musamman wadanda abin ya faru a gaban su. Wata Dattijuwa ce wacce a baya ta yi rayuwa irin ta zaman kai,har tsufa ya cimmata. Abinda mutanen garin su ka sani na zahiri, tsufa ne ya cimmata ta daina wannan Sana’a. Matar haka ta cigaba da rayuwar ta a gidan da ta mallaka, ta na sayar da yan kayan koli tana rayuwa. Duk Wanda ya taso zai sami tarihin na zaman karuwanci da ta yi. Ba ta shiga sabgogin mutane da yawa,amma ta kan je gaisuwar rasuwa ko barkar suna da sauran muamaloli.
Wataran wadanda ke makwabtaka da ita su ka jiwo Kakarin kamar tana Neman agaji. Sun same ta tana ta murkususu da alamun kamar cikin ta ke ciwo. Abin Mamaki matar babu abinda ke fita daga bakinta sai Kalmar shahada. A gabansu ta cika tana ta Kalmar Shahada. Kowa aka ba labarin yadda Matar nan ta cika sai ya rike baki,musamman wadanda su ka San lokacin da ta ke tashe a Bariki.
Wannan wani hukunci ne na ubangiji Wanda babu Wanda ya isa ya ce ma sa ya haka.
Mu koma kan Batun Malam Adam Zango.
Da farkon fara tashen Adam Zango,abinda aka fara jifansa da shi shine wai Musulunta ya yi. A addinance duk Wanda ya Musulunta laifi ne a dinga yi ma sa Gori,kuma duk Wanda ya Musulunta laifukan sa na baya ruwa ta sha,amma a wajen wa su ba haka ba ne.
Watan da ya shude na yi posting hotona da na Zango a wajen Maulidi. Da bayyanar Wannan photo sai Yan Izalar Facebook su ka hau suka, da maganganu iri iri. Ina sane bayan kwana biyu sai na yi posting din Hoton Zango da Wani Malamin Sunnah . Sheikh Ahmad Sulaiman. Na yi haka ne domin kuma na ji abinda za su CE.
Hoton na bayyana sai su ka ce ai daga gani Adam ne ya je a karu da Malamin domin ya wanke Kansa. Wasu kuma su ka ce ba Dan Allah ba ya dauki hoton Dan kawai a ce mai addini ne.
Irin wadannan mutane a ganin su wai addini su ke wa aiki. Abinda kuma ba su fahimta ba kamar su na taya shaidan aiki ne a kokarin su na tsarkake kawunan su da kuma Fasikantar da wani da baki.
Babu wani da aka yiwa umarnin binciko laifin wasu. Babu wani da Allah ya Dora masa dawainiya ta cin dunduniyar wani mai laifi ko Wanda ake zargin yana aikata laifi.
Jifan Wanda ake ganin ba bisa hanya yake ba da maganganun batanci da tozarci, babu wani amfani da ya ke yi illa kara jefa shi a rami. Mutanen da ke kiran kawunan su da Ahlussunah sun fi kowa irin wannan dabia ta muzanta Wanda su ke ganin bai bi irin hanyar da su ka bi ba.
Ina cikin Rubutun nan sai na ci karo da rubutun wani Matashin Dan Izalar nan Dan PDP Sabo Ahmad. Ga abinda yake fadi:
Ba a shiga hurumin Allah.
Kullum naga hoton bawan Allahn nan sai na qara sakankancewa da lamarin Allah.
Dalili kuwa shine: wannan bawan Allahn ajin mu daya a makaranta kuma abokina ne, kullum sai ya gaya min cewa babu abinda yake sha’awa kamar aikin SOJA, ni kuma sai in ce masa “Alqur’an baza a dauke ka Soja ba, Kalle ka fa ”
Abin mamakin ranar da ya fara aiki sai turo min hotunansa. Daga nan na fahimci kuskure na, har zuwa yau duk sanda muka hadu sai na tuna masa maganar sai kawai yayi dariya.
Wannan wata aya ce, cewa kada ka ta6a raina Dan Adam, Allah shine me yin yadda ya so da bawansa.
Allah ka gafarta mana laifukan mu.
Haka shima Wanda ke tunanin shi shiryayye ne, ta yiwu wataran ya tsinci Adam Zango ya zama Gogaggen Malamin Sunnah shi kuma ka tsince shi a layin Yan Rawar Malaja.
Abinda na ke son Matasan nan Yan Bana Bakwai su fahimci Allah ne kadai ke shiryar da Bawa. Ba kuma makale murya ko iya furta larabci ne shiriya ba.
Allah ya sa mu dace.
Daga Auwal Garba Danborno