Mujallar Bbc hausa ta ruwaito.
Wasu rahotanni sun ambato shugaban Amurka Donald Trump yana yin maganganun wulakanci kan 'yan ci-ranin da suka fito daga kasashen Haiti, El Salvador da Afirka ba. "Me ya sa wadannan mutane da suka fito daga wulakantattun kasashe suka shigo nan?" tambayar kenan da Mr Trump ya yi wa 'yan majalisar dokoki ranar Alhamis, kamar yadda kafafen watsa labaran Amurka suka ruwaito. Wadannan kalamai, wadanda ya yi a lokacin da suke tattaunawa kan shige-da-fice, ya yi su ne kan 'yan kasashen Afirka da Haiti da kuma El Salvador. Fadar White House ba ta musanta kalaman wulakancin da Donald Trump a kan 'yan ci-ranin ba. A makonnin baya bayan nan, gwamnatin Mr Trump tana ta kokarin ganin ta takaita iyalan 'yan ci-ranin da ke zaune a kasar da za a iya barin su su shiga Amurka, kuma ta dauki matakin ganin ta soke izinin zaman mutane da dama a kasar.
Mene ne takamaiman abin da ya fada?
Kalaman wulakancin da Mr Trump ya yi sun faru ne a lokacin da 'yan majalisar daga jam'iyyun kasar suka kai masa ziyara ranar Alhamis domin gabatar masa da kudirin dokar shige-da-fice wanda suka amince da shi. Dan majalisar dattawa na jam'iyyar Democrat Richard Durbin ya yi jawabi kan izinin zama dan kasa na wucin gadi da aka bai wa 'yan kasashen da suka hadu da mummunan bali'i. Jaridar Washington Post ta ambato Mr Trump na shaida wa 'yan majalisar cewa a maimakon karbar 'yan ci-rani daga wadancan kasshe, ya kamata Amurka ta rika amincewa da 'yan ci-rani daga kasashe irinsu Norway, kasar da Firai ministanta y ziyarci Trump a ranar. Jaridar ta ambato shi yana cewa : "Me ya sa za mu kyale 'yan kasar Haiti a wannan kasar? Ya kamata mu kore su."