LYRICS: BOC MADAKI YAWO


YAWO Lyrics By B.O.C(@BOCMadaki) [INTRO] Ji Mana,Ku Tsaya Guys!!! [CHORUS] Kyan Yawon Ba Tafiya Ba Ne,Dawowa Ne -Kyan Yawon Bayarwa Da Tarowa Da Kawowa Ne Kyan Yawon Ba Tafiya Ba Ne,Dawowa Ne -Kyan Yawon Bayarwa Da Tarowa Da Kawowa Ne -Lallai Kana Da Yawo! (Jama’a Suka Ce Mun) -Lallai Kana Da Yawo (Gayu Na Suka Ce Mun) -Lallai Kana Da Yawo (Babyn Chan Ta Ce Mun) -Lallai Kana Da Yawo [VERSE ONE] *What! *Da Muddun Na Bude Kofa,Na Shiga Mota *Bayan Direba Ya Anshi Boza *Kan Tafiya Ta Tabbata Da Addu’a Na Kan Soma *Domin Sai Da Rai A Kan Ci Oba *Ya Rabbi,Gatan Yara Da Manya *Makiyayin Mu Da Dare,Safe,Rana Da Yamma *Sa’in Da Muke Tafiye-tafiye Ka Kiyaye Mana Hanya *Gotta Get There Don Kar In Bar Iyaye Na Da Anya *Da Kiran Abokai Na A Waya Duk Don Su San Ya *Don Shi Ne Daya Daga Cikin Muhimmancin Kusanya *Bari Duk Wani Barawo Kar Ya Gan Mu *Kuma Duk Wani Tafiyan Da Muka Yi Mu Kai Da Ran Mu *Amen! Babu Abun Da Zan Ce Sai Dai Amin *Don Kamin Ma In Tambaya Uba Na Yana Min… -…Kyawawan Abubuwa *Kamar Bari Na Da Rai Da Sama Mun Batutuwa…. *….Na Fada Wanda Dan Adam Bai Tada Mun A Kunnuwa *In Dakata? Su Din Su Wa? [CHORUS] *Kyan Yawon Ba Tafiya Ba Ne,Dawowa Ne -Kyan Yawon Bayarwa Da Tarowa Da Kawowa Ne *Kyan Yawon Ba Tafiya Ba Ne,Dawowa Ne -Kyan Yawon Bayarwa Da Tarowa Da Kawowa Ne -Lallai Kana Da Yawo! *(Gyatuman Chan Ta Ce Mun) -Lallai Kana Da Yawo *(Dattijon Nan Ya Ce Mun) -Lallai Kana Da Yawo *(Mallam Hassan Ya Ce Mun) -Lallai Kana Da Yawo [VERSE TWO] *Komin Nisan Garin Ku Ku Shirya Don Muna Zuwa *Gara Mu Gaji,Mu Huta,Mu Tashi Da Mu Hakura *Don Da Hutu Ainun Bayan Mun Samu Babu Takura *Ga Ayawo,Ku Ce Wa Gayu Su Taru Fa *Ga Wuta,Toh Me Zai Hana Chasun Mu Faruwa *Gyatuma Ta Tana Mun Fata In Samu Gata A Rayuwa Ta *Da Na Ce ‘Amin’ Sai Na Ga Ko Ina Babu Rata *Kuma Karya Ne Rashin Arziki Ya Sa Mu Sata *In Har Na Taba Karaya A Da Yau Da Liver Na Dawo *Wasika Na Kawo *Sakon Da Ya Kunsa Shi Ne Yanzu Da Riba A Yawo *Tunda Kunnuwa Na Taimaka Wa Basiran Makaho *Mallam In Ka Tsani Kiwuya Sai Ka Diba Wa Yaro *Ka Mika A Baho *Domin Sai Iska Na Kadawa A Ke Shika Da Daro *Abun Kashedi,Ba Na Hira Da Tabo [CHORUS] *Kyan Yawon Ba Tafiya Ba Ne,Dawowa Ne -Kyan Yawon Bayarwa Da Tarowa Da Kawowa Ne *Kyan Yawon Ba Tafiya Ba Ne,Dawowa Ne -Kyan Yawon Bayarwa Da Tarowa Da Kawowa Ne -Lallai Kana Da Yawo! *(Aboki Na Ya Ce Mi Ni) -Lallai Kana Da Yawo *(Kawa Ta Ta Ce Mi Ni) -Lallai Kana Da Yawo *(Mabiya Na Suka Ce Mi Ni ) -Lallai Kana Da Yawo [VERSE THREE] *On My Way To A Destination Where My Destiny Leads *I’ve Seen So Many Nights With My Eyes Open *Survival Warfare,No Man Alive Is Resting In Peace *Tryna Make Something Real Outta All The Lies Spoken *Na Ga ‘No’,Na Ga ‘Biyayya’ – Na Ga ‘So’,Na Ga‎ ‘Kiyayya’ *I’ve Seen Love And Hate,I’ve Seen Curve And Straight *I’ve Seen Flop And Great,I’ve Seen Lords And Slaves *I’ve Seen The Highs And Lows,I’ve Seen The Thighs And Toes *Mallam Bar Ganin Ina Ta Hada Zufa *Sai Na Kai Inda Ba Wanda Ya Taba Zuwa *Fiye Da Jirgi Da Radio,Cike A Titi Da Stereo *Daba Daba Daban Daban,Tasha Tasha A Chan Da Nan *Mun San Hanyan Ba Kyau Amma Daga Kafa Alambaram *Always On The Road,Har Na Saba Da Gargada *Ai Cin Boris Ya Fi Kyau In Ka Chaba A Jar Kasa *Na Dawo Lafiya,Ga Saraba Ku Raba *Yau Yau Zan Koma In Ta Kama,Ko Da Kafa Mu Gwada [CHORUS] *Kyan Yawon Ba Tafiya Ba Ne,Dawowa Ne -Kyan Yawon Bayarwa Da Tarowa Da Kawowa Ne *Kyan Yawon Ba Tafiya Ba Ne,Dawowa Ne -Kyan Yawon Bayarwa Da Tarowa Da Kawowa Ne -Lallai Kana Da Yawo! *(Mutanen Bauchi Suka Ce Mun) -Lallai Kana Da Yawo (Mutan Arewa Suka Ce Mun) -Lallai Kana Da Yawo (Duk Nigeria Suka Ce Mun) -Lallai Kana Da Yawo
Previous Post
Next Post
Related Posts